ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa dubban mutanene suka fito zanga-zanga a birnin Bahir-Dar babban birnin Lardin Amhara da wasu garuruwan, inda suka yi allawadai da rikicin kabilanci tsakain kabilun Oromo da kuma Amhara, kabilu mafi yawa a kasar ta Habasha.
A cikin watan yuni mai zuwa ne za’a gudanar da zabubbuka na kasa a duk fadin kasar, don haka jam’iyyun siyasa sun fara yakin neman zabe don ganin sun kada jam’iyyar firai ministan kasar Abiy Ahmed
Rahotanni sun bayyana cewa a ranar litinin kadai mutane 18 ne ‘yan kabilar Oromo aka kashe a wani yanki a Lardin Amhara inda mafi yawan mazauna wurin yan kabilar Oromo ne.
342/